Kokarin kwato garin Mungonu | Labarai | DW | 26.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin kwato garin Mungonu

Rahotannin da ke shigo mana daga jihar Borno na cewar ana artabu da 'yan Boko Haram da dakarun rundunar sojin Najeriya a garin Mongonu da ya fadi a karshen mako.

Wani babban jami'ai a ma'aikatar tsaron kasar da ya zabi a sakaya sunansa ya ce sojin kasar na bakin kokarinsu wajen fattakar 'yan Boko Haram din duba da yadda ya ke da kusanci da Maiduguri, sai dai mutanen da suka tsere daga garin sun ce 'yan bindigar sun ja tunga a kokarinsu na cigaba da rike iko da shi.

Mazauna birnin Maiduguri sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewar suna jin amon manyan bindigogi daga bangaren da Mongonu din ta ke.