Kokarin korar ′yan Is a Iraki | Labarai | DW | 02.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin korar 'yan Is a Iraki

Mayakan da ke goyon bayan gwamnatin Iraki 28 ne suka hallaka yayin da wasu 34 suka samu raunuka a wani harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Baiji na kasar.

Wata majiyar tsaron kasar ta sanar da cewa dan harin kunar bakin waken ya tayar da bama-baman da ke jikinsa ne a wani Masallaci da Musulmi mabiya Shi'a ke taruwa domin karawa mayakan sa kai Kaimi a yakin da suke yi da 'yan kungiyar IS. Dama dai an saba fafatawa tsakanin 'yan ta'addan IS din da dakarun gwamnatin Iraki a birnin na Baiji cikin 'yan makwannin nan tare kuma da fuskantar hare-haren kunar bakin wake akai-akai daga mayakan na IS.