Kokarin kawo karshen rikicin Yemen | Labarai | DW | 15.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin kawo karshen rikicin Yemen

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya kaddamar da tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a Yemen.

Ban Ki-Moon yayin tattauna rikicin Yemen a Geneva

Ban Ki-Moon yayin tattauna rikicin Yemen a Geneva

A yayin da yake kaddamar da zaman tattaunawar sulhun a birnin Geneva na kasar Switzerland, Ban ya bukaci da a tsagaita wuta domin samun damar kai kayan agaji ga al'ummar da suka shiga halin tasku sakamakon hare-haren jiragen yakin rundunar taron dangi da Saudiyya ke jagorantar kaiwa a kasar. Sai dai a nasa bangaren ministan harkokin kasashen ketare na Yemen din Reyad Yassin Abdulla ya ce bai ga alamun hakan za ta samu ba, yana mai cewa tilas ne 'yan Houthi su fice daga biranen da suka kwace iko da su a kasar kafin a yi batun tsagaita wutar. Sama da mutane 2,600 ne dai aka tabbatar da cewa sun hallaka tun bayan da Saudiyya ta kaddamar da jagorantar yin ruwan bama-bamai a Yemen din.