Kokarin karbe iko da birnin Mosul | Labarai | DW | 29.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin karbe iko da birnin Mosul

Mahukuntan Iraki sun ce dakarunsu sun sake danna kai kudancin Mosul da nufin karbe ikonsa daga hannun mayakan kungiyar nan ta IS da ke rajin Girka daular Islama a wasu sassan kasar.

Ma'aikatar cikin gidan Irakin da ta tabbatar da wannan labarin ta ce sojin kasar sun dannan kai wannan yanki ne kuma sun fara da gundumar Intosar inda jami'an 'yan sanda da damar gaske tallafa musu wajen ganin sun kai ga nasara. Nan ba da jimawa ba inji ma'aikatar ta cikin gidan Iraki din jami'an tsaronsu za su samu nasara wajen karbe iko da baki dayan Mosul tare da tallafin mayakan Kurdawa da kuma sojin sa kai na masu bin tafarkin Shi'a a kasar.