Koffi Annan yayi kira ga ƙasashen dunia su bada hadin kai ga kwaskwarimar dokokin Majalisar | Labarai | DW | 12.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koffi Annan yayi kira ga ƙasashen dunia su bada hadin kai ga kwaskwarimar dokokin Majalisar

Sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, yayi kira ga ƙasashen dunia, masu ƙarfin tattalin arziki da masu tasowa, da su bada haɗin kai, domin cimma burin gudanar da kwaskwarima ga dokokin Majalisar.

A cikin wannan kira, Annan ya ce lokaci yayi, na ƙasashe su yi watsi da duk wasu manufofin san kai , muddun su na bukatar ganin wanan Majalisa ta taka rawar da ya dace da ita, a dandalin siyasa da na diplomatia na dunia.

Mahimman sauye-sauyen da su ka wajabta a kan Majalisar Ɗinkin Dunia, sun shafi ƙara ƙarfafa ci gaban ƙasashe, da tsaro, sannan a tabatar da kiyaye haƙƙoƙin bani adama, da kuma dokoki tafiyar, da ita kanta Majalisar, inji Koffi Annan.

A halin da a ke ciki akwai babban hadarin ƙarancin kuɗaɗen aiki, muddun ba a samu daidaito ba, tsakanin ɓangarorin masu jayyaya, a cikin shirye shiryen kwaskwarimar.