1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Kamaru: Ko ziyarar Fafaroma na da tasiri?

Zakari Sadou LMJ
April 16, 2026

Fafaroma Len na 14 ya samu kyakkyawar tarba daga dubban 'yan Kamaru wadanda suka mamaye titunan babban birnin kasar Yaounde, domin nuna farin cikinsu da ziyarar jagoran darikar Katolika mai taken zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/5CIpP
Kamaru | Yaoundé | 2026 | Ziyara | Fafaroma Leo na 14 | Paul Biya
Fafaroma Leo na 14 da shugaban kasar Kamaru Paul BiyaHoto: Simone Risoluti/Vatican Media/ABACA/picture alliance

A ci gaba da ziyarar da yake yi a wasu kasashen Afirka, Fafaroma Leo 14 ya aika babban sako ga hukumomin Kamaru ciki har da shugaban kasa Paul Biya mai shekaru 93 a duniya, inda ya ce duk da tsaro shi ne mafi muhimmanci ga kasa dole ne a tabbatar da shi ta hanyar mutunta 'yancin dan Adam. Bayan zaben shugaban kasa na 12 ga watan Oktoba 2025, gwamnatin Paul Biya ta murkushe zanga-zangar kin amincewa da sakamakon da ta haifar da cece-kuce.

Murkushe zanga-zanga da karfin tuwo

Zanga-zangar ta barke bayan da Biya ya lashe zabe karo na takwas da ta janyo asarar rayuka kuma da dama na tsare ba tare da wata kwakkwarar hujja ba galibinsu matasa, a cewar kungiyar lauyoyi da ke kare su. Kamaru da ke da kaso 35 cikin 100 na mabiya darikar Katolika, na fama da matsalar cin-hanci da rashawa. Duk kokarin da gwamnatin kasar ta yi na tsare wasu daga cikin mukarrabanta da aka samu da laifin cin-hanci, kawo yanzu wannan annonba na ci gaba da hana ruwa gudu a kasar.

Kamaru | Bamenda | 2026 | Ziyara | Fafaroma Leo na 14
Fafaroma Leo na 14, a birnin Bamenda na KamaruHoto: Guglielmo Mangiapane/REUTERS

Wannan ya sanya Fafaroma Leo na 14 cewa: "Dole ne mu tsinka sarkar cin-hanci." Jagoran darikar Katolikan ya ja hankali gwamnatin Kamaru da hadarin da ke tafe, muddin matasa ba su da ayyukan yi zai iya kawo rashin zaman lafiya ga kasa. A nasa bangaren shugaban Kamaru Paul Biya ya bayyana muhimmacin sakon zaman lafiya da babban limamin na mabiya darikar Katolita ke yadawa, a daidai lokacin da yakin Iran ya yi garkuwa da duniya.

'Yan aware sun bayar da hadin kai

'Yan awaren yankin da ke magana da Turancin Ingilishi na Kamaru, sun yi alkawarin dakatar da kai hare-hare na tsawon kwanaki uku don bayar da damar ziyartar babban taron adduo'i da Fafaroman zai gabatar a Bamenda da ke zaman babban birnin Arewa maso Yammacin kasarkana guda cikin yankuna da ke fama da tashe-tashen hankula tsakanin dakarun Yaounde da 'yan awaren da suka dauki makamai a shekara ta 2016 da kuma Douala cibiyar kasuwancin kasar da ake sa ran mutane 100,000 za su halarta.

 

Edited and published by Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani