1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zargi sakaci kan yaki da cin hanci

Zakari Sadou SB/LMJ
February 9, 2023

'Yan adawa sun soki gwamnatin Kamaru dangane da sakanci kan yaki da dabi'ar sama da fadi da dukiyar kasa. Wannan na zuwa ne lokacin da ake ci gaba da kama manyan jami'an gwamnati da ke zargi da almundahana.

https://p.dw.com/p/4NIOq
Kamaru I Shugaba Paul Biya
Shugaba Paul Biya na KamaruHoto: AP

Cin hanci da rashawa na ci gaba da samun gidan zama a kasar Kamaru bisa gazawar gwamnatin kasar da take cewa ta daura damara da yaki da duk wadanda suka yi sama da fadi da dukiyar kasa, sai dai kawo yanzu babu ci gaban da aka samu duk da kame-kamen da ake yi tsawon shekara da shekaru.

Ana danganta kame-kamen da neman kawar da duk masu yunkurin kwace mulkin Kamaru a hannun Paul Biya da ya kwashe shekaru 40 kan madafun ikon kasar. Shugaban kasar Kamaru Paul Biya da kansa ya ja hankulan al´ummar kasar a wani jawabi na bankwana da karshen shekarar 2022 a game da matakin ba gudu ba ja da baya a yunkurin kakkabe makarba rasahawa daga harakoki mulkin kasa.

Masu fashin baki a Kamaru na cewa matakin da kasar ta dauka tun tsawon shekara da shekaru na yakin da cin hanci wani salo na fakewa domin shiga sahun kasashe matalauta da za su ci gajiyar yafe bassukan da kasashen masu hannu da shuni su ka tambayo su. Cin hanci da rashawa, matsala ce da tayi kamari a Kamaru, tare da janyo cikas ga tattalin arzikinta da kuma yadda ake gudanar da ayyukan al'umma.

Kamerun Presse l Zeitungen l Symbolbild
Jaridun kasar KamaruHoto: Seyllou/AFP via Getty Images

Masana na ganin cewa, kudaden da aka yi sama da fadi da su daga 2006, a Kamaru ya zuwa yanzu, sun ninka biliyan sama da dubu. Kamaru na asarar biliyoyin kudi a duk shekara a sanadiyar cin hanci da rashawa. Su kuwa yan siyasa bangaren adawa na zargin gwamnati da laifin sakaci a yaki da take yi da rashawa.

Kisan dan jarida Martinez Zogo da ya yi fice kan shirinsa da yake gabatarwa wanda ke mayar da hankali kan yaki da cin hanci da rashawa ya bankado masu yi wasu lokuta har da ambata sunaye da ba da misalai da hujjoji wannan ne ya yi sanadiyar yi masa kisan wulakanci da cin zarafi.

Kisan dan jaridan ya tada hankulan jama'a da dama daga kungiyar kare hakkin 'yan jaridu ta Duniya Reporters Sans Frontiere da ke bin kididdigin lamarin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam zuwa 'yan siyasa ga gwamnatin kasar ta gaggauta gudanar da bincike kan kisan dan jaridan inda wasu suka kudiri aniyar maka gwamnatin kasar kotu saboda jinkiri wajen gudanar da bincike domin kama masu hannu dumu-dumu kan karkata kudin kasa yayin da mutane ke ci gaba da mutuwa sakamakon binciken da suke yi domin taimaka wa kasa.

Mutane da dama ba su yi amanna da kwamiti da gwamnatin kasar ke kafawa ba da sunan kwamitin yaki da cin hanci da rashawa.