Ko Kenya za ta yi shugabanni biyu? | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 02.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ko Kenya za ta yi shugabanni biyu?

Ikirarin madugun adawar Kenya Raila Odinga a matsayin shugaban al'umma, da kuma yunkurin Paul Kagame na tabbatar da ci gaban kasuwancin bai daya a Afirka a matsayin sabon shugaban AU sun dau hankalin jaridun Jamus.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a sharhinta mai taken "Rantsar da kai a Kenya" inda ta ce shugaban jam'iyyar adawa a Kenya Raila Odinga ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa. Watanni uku bayan sake gudanar da zabe mai cike da rudani a Kenya, shugaban jam'iyyar adawa Raila Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban al'ummar kasar. Sai dai gwamnati ta ce hakan ya saba doka. Wannan ne ya sa Mahukuntan kasar daukar matakin rufe wasu gidajen talbijin da radiyo. A karshen watan Oktoban shekarar da ta gabata ne dai aka sake zabar Uhuru Kenyatta a matsyin shugaban kasa bayan kotun kolin kasar ta soke zaben da ya gudana a watan Agustan shekarar da ta gabata din ta 2017 sakamakon wasu kura-kurai, sai dai Odinga ya ki shiga a fafata da shi a zaben na watan Oktoba, abin da ya bai wa Kenyatta damar lashe zaben.

Ruanda vor den Wahlen 2017 (Imago/Zumapress/M. Brochstein)

Sabon shugaban kungiyar AU, Paul Kagame

Ita kuwa a nata sharhin jaridar die tageszeitung cewa ta yi: "Yau Ruwanda gobe Afirka baki daya?" Ta ce shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya karbi ragamar jagorancin kungiyar Tarayyar Afirka AU da buri mai yawa. Yana fatan samar da Afirka mai budaddiyar kan iyaka "da kyakkyawan ci-gaba." Kagame ya ce tilas a hada hannu waje guda domin samar da ci-gaba mai ma'ana. A shekara ta 2017, yayin da yake matsayin shugaban kwamitin kawo gyara a kungiyar ta AU ya bukaci da a samar da Fasfo na bai daya a nahiyar da kuma batun kasuwanci mara shinge ta hanyar bude kan iyakokin kasashen Afirkan. A jawabinsa na karbar ragamar ta AU, ya sake gabatar da bukatar bude kan iyakoki na sararin samaniya a tsakanin kasashen nahiyar, inda ya ce ba da jimawa ba kasashen za su kasance suna yin kasuwanci mara shinge a tsakaninsu, ya kamata hakan ta kasance cikin wannan shekara ta 2018 da muke ciki domin samar da rayuwa mai inganci ga al'ummar nahiyar.

Äthiopien Addis Abeba Afrikanische Union Gipfel Guterres George Weah (Reuters/T. Negeri)

Shugaban kasar Laberiya, George Weah

A nata sharhin jaridar Neue Zürcher Zeitung mai taken "Weah ya kawo sauyi" ta ce sabon shugaban kasar Laberiya George Weah ya kawo gagarumin sauyi. A jawabinsa na farko Weah ya bayyana kudurinsa na cire ayar dokar da ke takaita bai wa bakaken fata 'yancin zama 'yan kasa a cikin kundin tsarin mulkin kasar. Tsohon dan kwallon kafar da ya yi rantsuwar kama aiki a ranar 22 ga watan Janairun da ya gabata, ya nunar da cewa zai bai wa 'yan kasar damar samun izinin zama 'yan kasashe biyu kana baki na da damar sayan filaye a kasar, ya kuma ce zai zaftare kaso daya bisa hudu na albashinsa. Wannan dai shi ne karo na farko da wata gwamanatin farar hula ta mika mulki ga wata gwamnati ta farar hula kana cikin ruwan sanyi a Laberiya tun daga shekara ta 1944. Tun dai a shekara ta 1847 ne Laberiya ta samu 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Amirka, sai dai Weah shi ne shugaban kasa na biyu a kasar da bai fito daga tsatson Amerikawa 'yan Laberiya ba.