Kizza Besigye dan siyasa ne na kasar Yuganda wanda aka haifa a shekarar 1956. Gabannin shigarsa harkokin siyasa ya taba yin aikin soja a kasar.
Besigye na daya daga cikin fitattun 'yan adawa Yuganda. Yunkurinsa na ganin an samu sauyin shugabanci a kasar ya sanya shi yin takarar shugabancin kasar har sau hudu wato a 2001 da 2006 da 2011 da kuma 2016.