Hana tofa albarkacin baki a Yuganda na karuwa | Siyasa | DW | 06.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hana tofa albarkacin baki a Yuganda na karuwa

Gwamnatin kasar Yuganda ta haramta kafofin yada labarai watsa zanga-zangar 'yan adawa kai tsaye, yayin da ake shirin sake rantsar da Shugaba Yoweri Museveni.

Yoweri Museveni Präsident Uganda

Shugaba Yoweri Museveni

Ranar Alhamis mai zuwa 12 ga watan Mayu za a sake rantsar da Shugaba Yoweri Museveni wanda ya shafe shekaru 30 kan madafun iko, amma tuni 'yan adawa suka sanar da jerin matakan da za su dauka da suka hada da zanga-zanga saboda nuna rashin amincewa da magudin da aka tafka yayin zaben watan Fabrairu. Ministan yada labarai Manjo Janar Jim Muhwezi ya tabbatar da haramta nuna zanga-zangar 'yan adawar kai tsaye:

"Mun tsayar saboda umurnin kotu wanda ya hana nunawa kai tsaye."

Babbar jam'iyyar adawa ta Forum for Democratic Change ta nuna tirjiya kan sake rantsar da Museveni kan madafun iko a wannan wata.

Kampala, Uganda Anhänger von Oppositionskandidat Kizza Besigye verbrennen Plakat von Yoweri Museveni

Zanga-zangar kin jinin shugaba Museveni

Yanzu gwamnatin Shugaba Museveni ta haramta zanga-zanga da hana kafofin yada labarai nunawa, a cewar ministan yada labarai Muhwezi:

"Idan akwai umurnin da ya hana Dr. Kizza Besigye wanda ya nuna tirjiya, idan aka ba shi damar magana kai tsaye ga duniya baki daya an saba umurnin ke nan."

Babban dan takara na adawa a zaben shugaban kasa Dr. Kizza Besigye na karkashin daurin talala saboda watsi da sakamakon zaben da ya bai wa Shugaba Yoweri Museveni nasara a watan Fabrairu.

Ugandas Oppositionsführer Kizza Besigye

Jagoran adawa Kizza Besigye

Masana shari'a a kasar kamar Nicholas Opio na watsi da matakin gwamnatin kan kafofin yada labarai.

Ita dai jam'iyyar adawa ta Besigye ta sha alwashi hana sake rantsar da Shugaba Yoweri Museveni kan madafun ikon kasar ta Yuganda.

Sauti da bidiyo akan labarin