Yuganda: Yoweri Museveni ya lashe zabe | Labarai | DW | 20.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yuganda: Yoweri Museveni ya lashe zabe

Shugaba Yoweri Museveni ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar Yuganda a ranar Alhamis din da ta gabata kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.

Hukumar zaben kasar ce ta ce Museveni ya samu kashi 60 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da babban mai hamayya da shi Kizza Besigye ya samu kashi 35 cikin 100.

Ya zuwa yanzu dai 'yan dawa ba su kai cewa komai ba game da sakamakon zaben na Yuganda, sai dai gabannin fitarsa 'yan adawar sun soki hukumar zabe da hada kai da hukumomi wajen tafka magudi.

Su ma dai wakilan kungiyar EU da suka sanya idanu kan zaben suka ce hukumar zabe kasar ba ta yin aikinta kamar yadda ya kamata a matsayinta na hukuma mai zaman kanta, kana sun nuna takaicinsu bisa yadda 'yan sanda suka yi amfani da karfi wajen kamewa tare da tsare madugun 'yan adawar Yuganda Kizza Besigye.