Kiristoci na yi wa Musulmai barka da soma azumi | Zamantakewa | DW | 18.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kiristoci na yi wa Musulmai barka da soma azumi

A wani mataki na neman kara zumunci da zaman lafiya shugabannin kiristoci sun aika gaisuwar barka da soma azumi ga Musulmai a Najeriya:

A wani mataki na neman kara karfafa huldar dangantaka tsakanin Musulmin Najeriya da kiristocin kasar,shumagabannin kungiyar kiristocin arewacin Najeriya ta CAN da limaman coci-coci da sauran mujami'un Najeriya,sun fara aika wa takwarorinsu malaman addinin muslunci da sauran Musulmin duniya gaisuwar taya su murna da zuwan azumin watan ramadan.

Farfesa Daniel Babaye magatakardan kungiyar kiristocin arewacin Najeriya ta CAN ya yi karin bayani.

Ya ce "Mu shugabannin kirista a arewa, kira muke yi ga 'yan uwanmu Musulmai cewa wannan lokaci na ramadan lokaci ne da ya kamata mu kebe kanmu a zauna a yi karatun kur'ani da addu'o'i, a yi azumi domin Ubangiji Allah ya sada mu da rahamarsa".

Har wa yau dai kungiyar kiristocin arewacin Najeriyar ta gargadi 'yan kasuwa kan illar tsauwala wa al'ummar kasa tsadar kayayyakin masarufi.

Shiko Pasto Yohana Buru shugaban cocin Kirist Evangelical intercessary fellowship a Najeriya,kamar ko wace shekara ya saba 'yanto firsinoni Musulmai da zummar ganin sun yi azumi a gida da iyalansu,a wannan shekara ma dai ya 'yanto Musulmin masu yawan gaske tare tare kuma da rarraba wa masu zaman kurkukun abincin buda baki.

Ya ce "ina wa 'yan uwana Musulmai duk ko ina suke a duniya fatan alkhairi da fatan su fara wannan azumi lafiya su gama lafiya a kuma samu falalarta da albarkatun da ke a ciki.Kuma muna shirin tsara budabaki da Musulmi,sannan firrsinoni dama nakasassu za mu kai masu abinci na buda baki da nufin kara dankwan zumunci tsakanin mu kristoci da 'yan uwanmu Musulmai.

Su kwa kananan 'yan kasuwa koka wa suka yi da yanda manyan 'yan kasuwa masu sayan kayan gwari da na masarufi a parashi mai sauki amma suke sayar masu da tsada. Daga nasu bangare malaman Muslunci sun gudanar da kiraye -kiraye a kafofin yada labarai kan kauce wa yin miyagun kalamai na nuna kyama ga wani rukuni na al'umma domin ganin an samu zaman lafiya a tsakanin al'ummar kasar ta Najeriya