Kira ga soma aikin hadin kai a Libiya | Labarai | DW | 19.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kira ga soma aikin hadin kai a Libiya

Kasashen duniya da dama sun yi kira ga bangarorin Libiya da su gaggauta sanya hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kann kasa da suka cimma tsakaninsu.

Kasashen duniya da dama sun yi kira a wannan litanin ga bangarorin da ke gaba da juna a kasar libiya da su gaggauta sanya hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan 'yan kasa da suka cimma a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya .

Kasashen da suka hada da Amirka da Tarayyar Turai da na Larabawa sun sanya wannan kira ne a cikin wata sanarwar hadin guywa da suka fitar a wannan Litinin a birnin Paris inda suka ce a shirye suke su kawo goyon bayansu ga gwamnatin hadin kan kasar Libiyar dama kawo mata dauki a fannin yaki da ayyukan ta'addanci.

Ranar tara ga wannan wata na Oktoba ne bangarorin da ke gaba da juna a kasar ta Libiya suka cimma matsaya kan sabuwar gwamnatin hadin kan kasar mai kunshe da mambobi 17 a karkashin jagorancin Firaminista Fayez el-Sarraj. Sai dai har kawo yanzu babu bangaren da ya saka hannunsa a kan yarjejeniyar a hakumance.