Keir Starmer da Ahmed al-Sharaa sun magantu a Burtaniya
March 31, 2026
Shugaba Ahmed al-Sharaa da mai masukinsa Starmer sun tattauna kan muhimman batutuwan da suka tayar da kura a duniya, kama daga batun yankin Gabas ta Tsakiya da na yakin Iran da Amurka da Isra'ila har da batun mashigin ruwa ta Hormuz da Iran ke ci gaba da yi wa tsayin gwamin jaki.
Merz da Sharaa sun amince da aiki tare kan 'yan hijira
Kakakin fadar firaministan Burtaniya, ya ce wani muhimmin batun da bangarorin biyu suka zanta har da na 'yan gudun hijirar Siriya a Burtaniya da makomarsu, kafin daga bisani Shugaba al-Sharaa ya kai ziyarar ban girma a fadar Sarki Charles III
Wannan ita ce ziyarar farko da shugaban Siriya ya kai a Burtaniya, tun bayan dawo da alakar kasashen biyu a cikin watan Yulin 2025, jim kadan bayan karbe iko daga gwamnatin Bashar al-Assad da ta jima tana 'yar tsama da kasashen yammacin duniya a shekarar 2024.
Jamus ta jaddada yunkurinta na mayar da bakin haure 'yan Siriya a gida
Siriya da Burtaniyya sun sanar da shirinsu na ba wa kamfanonin Burtaniya damar samun kwangila da farfado da muhimman ayuukan raya kasa a Siriya kamar yadda sanarwar ta sanar.