Kebbi: Wata ta kubuta cikin daliban da aka sace
November 18, 2025
An sace dalibban mata ne a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari a wata makarantar Sakandaren 'yan mata da safiyar litanin ta wannan mako da misalin karfe 4, inda suka yi awon gaba da wadannan 'yan mata 25, kana suka kashe mataimakin shugaban makarantar da wani maigadi.
Dalibar da ta gudo daga cikin daji 'yan sa'o'i bayan satar a makarantar Government Girls Comprehensive Secondary School, in ji Musa Rabi Magaji, shugaban makarantar.
Sace-sacen dalibbai ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya inda kungiyoyin 'yan bindiga da masu ikirarin jihadi suke gudanar da wannan aiki, Kuma galibi makarantu ne 'yan bindigar suka fi mayar da hanakali kamar yadda masana ke cewa.
Kawo yanzu dai ba bu wata kungiya da ta dauki alhakin wannan aika-aika.
Ko a shekarar 2021 wasu 'yan bindiga sun sace dalibbai mata a makaranatar mata a karamar hukumar Yawuri ta jihar Kebbi.
Masu sharhi na zargin cewa karuwar cin hanci da rashawa ya kawo nakasu ga samar da wadataccen makamai ga Jami'an tsaro abin da ake zargin ya haifar da karuwar hare-hare.