1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu: Karshen mulkin wariya

June 30, 2021

Shekaru 30 ke nan da kawo karshen mulkin wariyar launi fata a Afirka ta Kudu. An dai soke dokar mulkin wariya launin fata na tsirarun Turawa a kan bakar fata, a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 199.

https://p.dw.com/p/3vpnZ
London Wembley Stadion "Free Mandela" Konzert
Zanga-zangar neman sako Nelson Mandela daga gidan kasoHoto: picture-alliance/ dpa

An dai soke dokar mulkin wariya launin fatar a Afirka ta Kudu, shekara guda bayan sakin marigayi tsohon shugaban kasar da ya jagoranci gwagwarmayar yaki da wariyar launin fatar, Nelson Mandela daga gidan kaso. Sai dai duk da cimma wannan matsayi, har yanzu a fili take ana fama da wariyar launin fatar a kasar. Sama da kaso biyu cikin uku na yawan al'umma bakar fata na rayuwa cikin taluci da kunci, yayin da kaso guda ne kacal na farar fatar kasar ke cikin talauci.

Karin Bayani: Kalubalen siyasa da tattalin arzikin Afirka ta Kudu

Mmapula Minisi masani a kan harkokin rayuwa, ya ce an samu ci gaba sai dai da sauran aiki har yanzu: "Tun lokaci da aka soke dokar wariyar launin fatar, bakatar fata na samun wasu abubuwan rayuwa ba kamar a baya ba. Misali illimi kana yanzu za ka iya zuwa wuraran shakatawa cikin shaguna. An nada bakake da dama a matsayi na manyan jagorori a kamfanoni da masana'antu. Amma akwai kalubale a kan batun zaman kashe wondo da ilimi da kiwon lafiya da samar a muhalli. Bayanai na kididiga da hukumar yin daidaito wajen samar da aiki ta yi, ya nuna cewar mukamai na manyan daraktoci har yanzu suna hannun farar fata, duk da cewar ba su wuce kaso tara cikin 100 na al'ummar Afirka ta Kudu ba, amma kusan kaso 64 cikin 100 na manyan mukamai sune ke rike da su."#b#

Nelson Mandela 100 Jahre
Jagoran gwagwarmayar yaki da wariyar launin fatar Afirka ta Kudu Nelson Mandela Hoto: picture-alliance/dpa/J. Hrusa

'Yan gwagwarmaya irin gwarzo Nelson Mandela da Steve Biko da ma wasu farar fatar masu goyon bayan bakar fata kamar Denis Gold Berg. Faman da suka yi na tsawon sama da shekaru 30, shi ne samar da daidaito a tsakanin al'ummar Afirka ta Kudu. Masu yin sharhi a kan al'amura na cewar, akwai sakacin gwamnatocin da suka mulki kasar. A cewar Trevor Ncube wani masanin tattalin arziki, akwai matakai uku da aka yi sake da su da suka hadar da ilimi da cin hanci da almundahana da kudin al'umma, wadanda sune suka kawo jinkirin kawar da bambancin kwata-kwata.

Karin Bayani: Jan aiki a gaban sabon shugaban ANC

Afirka ta Kudu dai ta kasance daya daga cikin kasashen duniya da ake nuna fiffiko da bambanci mafi girma a cewar wani rahoton Bankin Duniya, duk da cewar a shekarun baya-bayan nan ana damawa da bakar fatar a harkokin yau da kullum na rayuwa. Tun da fari dai jam'iyyar da ke mulki a kasar ta ANC ta yi alkawari samar da kyakyawar rayuwa ga al'umma cikin sauyi na samar da daidaito ta fanin illimi da kiwon lafiya da albashi da sauransu, amma wani bincike na baya-bayan nan da kungiyar Oxfam ta gudanar, ya nunar da cewa galibin mata bakar fata albashinsu ya bambanta da na fararen fata wadanda ake ninka musu albashi fiye da sau 460 a kan bakar fata masu manyan mukamai.