1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen siyasa da tattalin arzikin Afirka ta Kudu

Lateefa Mustapha Ja'afar AMA
April 26, 2019

Bayan wani tsawon lokaci ana fama da bambance-bambance, kasar Afirka ta Kudu ta gudanar da zaben da ya kawo karshen mulkin fararen fata da mulkin 'yan tsiraru a shekarar 1994.

https://p.dw.com/p/3HWr1
Nelson Mandela 100 Jahre
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Hrusa

Shekaru 25 ke nan tun bayan da aka zabi Nelson Mandela a matsayin shugaban kasar Afirka ta kudu, zaben da ke zaman na farko da aka gudanar a ranar 27 ga watan Afrilu na shekarar 1994 ya kawo karshen gwagwarmayar mulkin nuna wariyar launin fata a kasar ta kudancin Afirka. A yanzu shekaru 25 bayan tsalle da murna, sai ga shi matsalar rashin aikin yi da karancin ilimi na neman yin kaka gida a kasar baya ga fama da kalubale a fannin siyasa da na tattalin arziki duk da yake tsohon shugaban kasar Nelson Mandela, ya yi nashi kokarin na ganin komai ya daidata.

Kasar Afirka ta Kudu na fama da gagarumar matsalar cin hanci da rashawa a tsakanin mahukuntanta inda masana ke cewa biliyoyin kudin kasar da yawa ne mahukuntan suka yi sama da fadi da su domin amfanin kansu maimakon tallafa wa talakawa da aka kiyasta sun kai kashi 79 cikin dari yin fito- na-fito da talauci da ke zaman babban kalubale da kasar ke fama da shi a yanzu.

Masu sharhi na tofa albarkancin bakinsu kan Afirka ta Kudu

Südafrika Flagge vor Tafelberg, Kapstadt
Hoto: picture-alliance/dpa/Bildagentur-online/Fischer

Thembinkosi Dlamini daga jami'ar Oxfam ta Afirka ta Kudun na da kwarin gwiwa kan yadda kasar za ta kasance a gaba, yana mai cewa batun talaucin da ake fama da shi na da nasaba da bambancin da ke tsakanin masu kudi da talakawa a wannan kasa.

 "Ba zan ce an cimma fatan da Nelson Mandela ke da shi ba, amma ana ci gaba da tafiya. Kai tsaye, ba za mu ce mun yi watsi da fatan da ake da shi mun koma gidan jiya ba. Abin da muke gani a yanzu bayan sauya gwamnati, shi ne al'umma na jagorantar shugabannin da ke da ra'ayin tinkarar kalubalen da Afirka ta Kudu ke fuskanta. Misali, abin da muke ganin a mulkin Shugaba Cyril Ramaphosa kamar tsananin akidarsa ta yaki da cin hanci da rashawa da burinsa na farfado da hukumomin gwamnati domin su fara aiki yadda ya kamata."   

Yanzu lokaci ne da ya kamata a tuna da dalilan gwagwarmayar da Nelson Mandela ya yi a can baya da ma ra'ayin hukumar sasantawa da aka kaddamar domin tabbatar da adalaci tsakanin 'yan kasa, wadda kuma ta gabatar da cikakken rahoto da ra'ayoyi kan yadda za a bunkasa dimukuradiyyar kasar ta Afirka ta Kudu.