Kawar da Makamai masu guba a Siriya | Labarai | DW | 02.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kawar da Makamai masu guba a Siriya

Kwararrun kasa da kasa kan kwance damarar yaki sun isa fadar gwamnatin Siriya watau Damaskus, domin fara nazarin kawar da makamai masu guban kasar.

Jami'ai 19 daga kungiyar dake haramta amfani da makamai masu guba dake da cibiyar ta a birnin The Hague na kasar Nethrlands ne dai suka je Damaskus, yini guda bayan ficewar jami'an Majalisar Dunkin Duniya da suka tabbatar da amfani da makamai masu guba a kan jama'a. Ana saran kwararrun za su aiwatar da kudurin komitin sulhu na Majalisar, na bada umurnin kawar da makamai masu guban, wanda yawansu ya kai 1,000 daga yanzu zuwa tsakiyar shekara mai zuwa. Sai dai ministan yada labaru na Siriyan ya jaddada cewar, shugaba Basha al-Assad zai ci gaba da kasancewa kan karagar mulki, kuma yana iya yin takara a zaben kasa na shekara mai zuwa, idan har yana muradin yin hakan. Daya daga cikin bukatun 'yan tawayen kasar dai shine, Assad ya bar mulki. Nan da makonni biyu masu zuwa ne bangarorin biyu za su hadu a taron sasanta kasar a birnin Geneva.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu

I