Kasashen Turai sun ja kunnen Amirka | Labarai | DW | 12.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Turai sun ja kunnen Amirka

Wasu daga cikin manyan kasashen Turai sun yi kira ga shugaban Amirka Donald Trump da ya martaba yarjejeniyar da aka cimma dangane da makamin nukiliyar Iran.

Kasashen dai na wannan kiran ne yayin da ake sa ran shugaban na Amirka zai sanar da takunkumi ga Iran din. A baya dai tsohon shugaban Amirka Barack Obama ya amince da yarjejeniyar, wacce shugaba Trump ya soma ja a kanta jim kadan da hawarsa karagar mulkin Amirkar.

Manyan kasashen duniya da suka hada da Jamus da Faransa da Birtaniya da China da Rasha da ma Amirka ne dai suka amince wa Iran din mallakar makamin na nukiliya. Sakataren Baitul malin Amirka ya fada jiya Alhamis, cewar akwai yiwuwar Mr. Trump ya bayyana jerin takunkumi kan Iran a yau Juma'a.