Kasashen duniya na adawa da juyin mulki a Burundi | Labarai | DW | 14.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen duniya na adawa da juyin mulki a Burundi

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zauna a ranar Alhamis din nan dan tattauna rikicin da ke faruwa a Burundi yayin da kungiyar AU ma ta yi Allah Wadai da karbar mulkin da karfin soji.

Adaidai lokacin da fada ke ci gaba da rincabewa a birnin Bujumbura bayan da wani janar din soji ya bayyana juyin mulki a wannan kasa. A wani bangare kuma wasu rahotanni na cewa shugaban kasar Pierre Nkurunziza na boye a wani waje a Tanzaniya.

Da yake jawabi ga jami'an diplomasiya a birnin Nairobin Kenya Said Djinnit wakilin Sakataren Majalisar ta Dinkin Duniya, ya ce yana duba hanyar komawa birnin Bujumbura fadar gwamnatin kasar ta Burundi dan ganin lamarin bai kazance ba.

Djinnit ya fadawa wani zaman kwamitin da aka yi cikin sirri cewa ana ci gaba da ruwan alburusai a birnin yayin da hedikwatar yada labarai ta kasar ke fargabar fisakantar hari da makaman roka.

Ita ma dai kungiyar kasashen Afrika ta AU ta yi Allah wadai da yunkurin kwace mulkin kasar ta Burundi da karfin soji, inda ta bukaci a gaggauta koma wa warware rikicin kasar a siyasance.

Amina Diallo Djibo da ke zama jakadar kasar Nijar kuma shugabar kwamitin na zaman lafiya daga kungiyar ta AU ta yi karin bayani kamar haka:

"Kwamitin zaman lafiyar na PSC da kakkausar murya ya yi Allah wadai da duk wani yunkurin kwace mulki ta hanyar amfani da karfin tuwa ba ta hanyar lalama ba".