1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ramaphosa ya jagoranci shirin dakatar da yakin Turai

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
June 2, 2023

A kokarin kasashen Afirka na lalubo hanyar kawo karshen yakin Rasha da Ukraine, shugaban kasar Afirka ta Kudu ya tattauna da Shugaba Putin da Zelenskyy.

https://p.dw.com/p/4S89I
Shugaba Ramaphosa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin
Shugaba Ramaphosa da takwaransa na Rasha Vladimir PutinHoto: Mikhail Metzel/ITAR-TASS/IMAGO

Kasashen Afirka na kokarin lalubo hanyar kawo karshen yakin Rasha da Ukraine, inda tuni shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna da Shugaba Vladimir Putin na Rasha da takwaransa Volodymyr Zelenskyy na Ukraine kan wannan batu. Yakin Ukraine din ya janyo matsalolin samar da abinci a kasashen Afirkan, wadanda suka dogara da Ukraine domin samun alkama.

Wannan wani mataki ne da ya bai wa kowa mamaki, in da aka samu kasashe shida na Afirka da suka hadar da Senegal da Yuganda da Zambiya da Kwango Brazzaville da Masar da kuma Afirka ta Kudu suka bayyana aniyarsu ta shiga tsakani domin kawo karshen yakin na Ukraine.

Kasashen Afirka na dogaro da kayan hatsin Ukraine
Kasashen Afirka na dogaro da kayan hatsin UkraineHoto: Prabhat Kumar Verma/Pacific Press/picture alliance

Sai dai ana saka ayar tambaya kan ko Afirka ta Kudu ka iya taka rawa ta shiga tsakani, ganin irin dangantakar da ke tsakaninta a da Rashan. Amurka ta ma zargi Afirka ta Kudun da taimakawa Rashan da makamai tana mai cewa, makaman sun isa sansanin sojojin ruwan Rasha a watan Disambar bara, zargin da Pretoria ta musanta. Ministan harkokin waje na Rasha Sergey Lavrov  ya nunar da cewa, Chaina ce kadai ta fitar da wani tsari na kawo sulhu, inda a yanzu take jiran tsarin da Afirka da Brazil za su fitar. A kokarin da yake na inganta dangantaka da Afirka, Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine, ya sha alwashin bude karin ofisoshin jakadancin kasarsa a nahiyar.

An shafe fiye da shekara daya da barkewar yakin Rasha da Ukraine
An shafe fiye da shekara daya da barkewar yakin Rasha da UkraineHoto: Russia/Ukraine Press Offices/AP/picture alliance

Masu fashin baki dai na ganin a ina Afirkan za ta samu karfin gwiwar shiga tsakani a yakin da ke gudana a Turai, tare da yin watsi da tarin rikicin da ake fama da shi a nahiyar? Sun dai gaza shawo kan rikicin da ke faruwa kamar na kasashen Habasha da Sudan, wanne fata suke da shi na kawo sauyi a Ukraine?

Yakin na Ukraine dai ya bar kasashen Afirka da dama cikin wani yanayi na banbarakwai, a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya. Mafi yawansu sun zabi su kauracewa kada kuri'a, yayin da ake kokarin yin tir da mamayar Rasha a Ukraine. Sai dai ta yiwu dalilin kasashen Afirkan na ganin an kawo karshen yaki, na da alaka da yanayin da nahiyarsu ke ciki. Yakin ya ta'azzara matsalolin karancin abinci da man fetur da ma tsadar rayuwa a kasashe da dama, abin da ya sanya shugabanni ke neman mafitar da sulhu a Ukraine ka iya kawo wa ga kasashensu.