Kasashe za su ceto dajin Amazon | Labarai | DW | 25.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe za su ceto dajin Amazon

Shugabannin kasashe bakwai masu karfin arziki da ke taro a Faransa, sun amince da taimaka wa kasashen da ibtila'in gobarar dajin nan na Amazon ta shafa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya yi jawabi kan gobarar a wannan Lahadi, ya ce ya zama wajibi a sama wa kasashen taimako cikin gaggawa, hasali ma an yi nisa wajen tuntubar kasashen.

Kungurmin dajin na Amazon dai, na da muhimmancin gaske ga duniya, ta fannin samar da iskar oxygen da ake shaka da yaki da dumamar yanayi, don haka ne ma bukatar sake dawoda shuke-shuken da ke a wajen ya dauki hankali.

Shi kuwa shugaban darikar Katholika na duniya, Fafaroma Francis, kira ya yi ga kasashen duniya da su hada karfin ganin an kashe wutar da ke ci gaba da ci a dajin na Amazon da ke a Brazil.