1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rufe iyakoki da matakan kandagarki kan cutar corona

Abdourahamane Hassane
March 18, 2020

Kasashe na baya bayan nan da suka hada da Jamhuriyar Nijar da Kamaru sun bayyana rufe iyakokinsu tare da rufe makarantun firamari da sakandare da kuma jamio’i a sakamakon annobar ta corona.

https://p.dw.com/p/3ZdP0
Deutschland Frankfurt am Main Flughafen | Coronavirus
Hoto: Getty Images/AFP/T. Silz

Kamaru ta dauki matakin ne bayan gano karin wasu mutane biyar da ke dauke da kwayar cutar. Ta soke gasar cin kofin kwallon kafa na  nahiyar Afirka da za a yi a kasar a wannnan shekarar, yayin da ake sa ran Afirka ta Kudu za ta rufe iyakokinta. Haka ma Tunisiya da Moroko sun dakatar da zirga zirgar jiragen sama har sai abin da hali ya yi tare da haramta wa yan kasahen da ke dauke da kwayocin cutar shiga cikin kashensu. yayin da Chadi da Sudan da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya suma suka dauk irin  wannan mataki.

Shin ko rufe iyakoki zai iya zama riga kafi na kamuwa da cutar ? Soumaila Dagnako shugaban wani gida rediyon ne na karara da ke tsakain Burkina Faso da Mali da Cote d'ivoire.

Afrika Sambia Coronavirus Vorkehrungen
Wani da ya je sayen abin rufe baki da hanci a shagon sayar da magani a kasar ZambiyaHoto: picture-alliance/AP Photo/E. Mwiche

Yace a  Hukumance za a iya cewar an rufe iyakar amma a zahiri abu ne mai wuya ga hukumomin su martaba wannan doka ta ko ina daga wata kasa kana iya zuwa wata ace misali daga Mali za ka iya zuwa Cote d Ivoire daga Mali ka je Burkina Faso ba ma cikin ka sani ba

Yunkurin gwamnatoci wani abu ne na nunawa duniya cewar sun damu da kiyaye lafiyar al’umominsu amma duk da haka wasu jama’ar sun yarda da matakan da shugabannin ke dauka. Kassim Windea wani dan kasar Rwanda ne.

Afrika Senegal Coronavirus Pasteur Institute in Dakar
Cibiyar binciken cutattuka a kasar SenegalHoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Yace ba mu san ta inda kwayoyin cutar na corona za su shiga kasarmu ba ta sama ne ko kasa, ba mu sani ba. Abin da ya fi shi ne yin riga kafi kafin cutar  kafin ta zo nan, ina tsamanin yana da kyau hukumomin su kara daukar matakai domin hana cutar kutsa wa cikin kasarmu.

Ko da shike abubuwan sun sha bamban a lokacin da cote divoire ta yi kokarin  rufe iyakarta a mali a shekara ta 2012 bayan juyin mukin janar Amadou Sonogo abin ya gaza yiwuwa don jama’a sun ci gaba da kai da kawo a tsakanin kasashen sakamakon yada rayuwar al’umar kasashen da ke bakin boda ta zama daya