Kasar Saudiyya ta fille kawunan mutane uku | Labarai | DW | 17.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Saudiyya ta fille kawunan mutane uku

Gwamnatin Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa a kan wadanda aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi da kuma kisan kai.

Hukumomin Saudiyya sun aiwatar da hukuncin kisa ta hayar fille kai a kan wasu 'yan kasar biyu da kuma dan Pakistan daya da aka samu laifin safarar miyagun kwayoyi da kuma kisan kai. A cikin watanni uku na baya-bayannan dai mutanen 48 aka aiwatar da hukuncin kisa a kansu a Saudiyya, adadin da ya ninka idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Ma'aikatar cikin gida ta wannan kasa ta ce an fille wa Mumtaz Hussein dan kasar Pakistan kai da takobi a birnin Madina da ke yammacin kasar, yayin da su 'yan kasar uku kuma aka aiwatar da shari'ar a kansu a birane daban daban ciki har da Taef da ke shi ma ke yammacin saudiyya.

Tun dai watan Satumban bara ne, wani kwararre na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana fargaba dangane da tsarin shari'a da saudiyya ke amfani da shi musamman ma hukuncin kisa . Ita dai Saudiyya ta na ci gaba da aiwatar da hukunci kisa a kan duk wanda aka samu da laifin fyade ko kisan kai ko fashi da makami ko yin ridda ko kuma saye da sayar da miyagun kwayoyi.