kasar Iraki ta kama ′yan IS 500 a Fallujah | Labarai | DW | 13.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kasar Iraki ta kama 'yan IS 500 a Fallujah

A wata fafatawar da suka yi tsakaninsu da nufin karbe iko da garin Fallujah ne jami'an na iraki suka yi nasarar kama masu kaifin kishin Islama na kungiyar IS.

Jami'an tsaron kasar Iraki sun tsare sama da mutane 500 da ake zargi da zama 'yan kungiyar IS, a lokacin da suke sajewa da fararen hula da ke yunkurin ficewa da a birnin Fallujah da mayakan ke iko da shi.

Sama da fararen hula 50,000 ne mayakan na IS suke garkame da su a tungarsu kafin dakarun gwamnati su kai dauki da ya kubutar da fararen hulan zuwa sansanin da gwamnati ta tanadar.

Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da dakarun gwamnatin Irakin ke ikirarin samun nasaran karbe iko da birnin na Fallujah da ke zama babbar sansanin na mayakan na IS, kamar dai yadda wani jami'in tsaron kasar ke cewa.

"Baya ga gagarumin taron dangi da muka yi wa mayakan, rundunar 'yan sanda su nyi nasarar tarwatsa tungar da suke ji da shi. Kuma da haka ne muka samu nasara a kan su."

Shekaru biyu kenan da mayakan na IS ke rike da iko da birnin na Fallujah.