Kasar Amurka na neman ganin an gaggauta wanzar da kudurin MDD domin daukar matakai na takunkumi akan kasar Iran… | Labarai | DW | 08.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Amurka na neman ganin an gaggauta wanzar da kudurin MDD domin daukar matakai na takunkumi akan kasar Iran…

Amurka tayi kira da a gaggauta wanza da kudurin kwamitin sulhu na MDD da ke da alhakin kakabawa Iran takunkumi cikin mako mai zuwa. Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Nicholas Burns fada cewar a ranar litinin mai zuwa za’a yi zaman tattunawa tsakannin gaggan kasashennan 6 dake da cigaban tattalin arziki, wadanda ke neman cimma daidaituwa da Iran aka shirinta na nukiliya. Wannan ya biyo bayan wata tattaunawa ce tsakannin manyan jami’ai da aka yi a jiya alhamis a birnin Berlin, inda suka tattauna batun nukiliyar kasar ta Iran. Anyi sati daya da Iran ta yi watsi da wa’adin da MDD ta bata na ta dakatar da harkokin da take yi na mallakar makamashin nukiliya. Amma kawo yanzu ba’a cimma daidaituwa akan kakaba wa kasar takunkumi ba, sabili da wasu kasashe dake da wakilci a kwamitin sulhu na MDD, irin su China da Rashiya dake dari-dari da lamarin.