Karuwar rikicin manoma da makiyaya | Siyasa | DW | 19.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Karuwar rikicin manoma da makiyaya

A Najeriya yanzu haka babban matsalar tsaro da kasar ta fi fiskanta shi ne batun wuraren kiwo da masu gonaki, inda ake yawaitar samun tashe-tashen hankula

Wani mummunan tashin hankalin da ya tashi sakamakon jayayyar filin noma, a wasu kauyuka da ke a yankin Zuru ta jihar Kebbi, ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 15. Gwamnatin jihar Kebbi da rundunar 'yan sanda ta jihar, duka sun tabbatar da aukuwar rikicin, wanda ya samo asalin akalla shekaru 10 da suka gabata, kuma ake ci gaba da shari'a a gaban kuliya tun a wacan lokacin kawo yanzu. A halin da ake ciki yanzu haka al'amura sun lafa, a wannan yankin da ke a karkashin kulawar jami'an tsoro.

A bisa kokarin shawo kan wannan matsalar, kungiyar fulani makiyaya a Najeriya da aka sani da Mi Yetti Allah, ta kira wani taron karawa juna sani, domin duba yadda za'a shawo kan matsalolin, mumman yadda ake samun barayin shanu, lamarin da kan jawo ramuwa, abinda ke rikidewa zuwa fadan kabilanci. A Yanzu haka a Najeriya dama sauran kasashen Yammacin Afirka, mutane da yawa ke rasa rayukansu sakamakon rikicin makiyaya da manoma.

Masana a Najeriya sun gano cewa, karewar dazukan jihohin Arewa da karuwar kwararowar hamada, tare da zaizayar kasa na ci-gaba da zama wasu daga cikin man'yan matsalolin da ke tursasa makiyaya, yin gudun hijira da dabbobin su. Inda suke tashi daga Arewacin kasar zuwa kudancin kasar ko ma su tsallaka izuwa kasashe makobta, domin samun wuraren kiwon dabbobinsu.

Sauti da bidiyo akan labarin