1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kokarin maganta matsalar garkuwa da mutane

Uwais Abubakar Idris
October 28, 2019

Mahalarta taro kan matsalar garkuwa da mutane a karkashin gidauniyar Friedrich Ebert sun shawarci gwamnati da ta tsara manufa ta bai daya domin shawo kan matsalar da ke kalubalantar yanayin tsaron kasar.

https://p.dw.com/p/3S6Ek
Nigeria Polizei
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Duk da sanin cewa garkuwa da jama'a babban laifi a Najeriyar amma sannu a hankali ta zama tamkar wata sana'a da ke jan hankali matasa, mata da ma yara kanana saboda lasa gardin makudan kudin da ake samu.

An dai yi mawara sosai a kan ko tsarin yiwa masu garkuwa afuwa ka iya zama mafita, inda kwararru suka yi itifaki da cewa ai afuwa ma gazawa ce ga gwamnati, domin in da tana tasiri da an ga hakan a yankin Niger Delta. Hajiya Hadiza Sani Kangiwa jami'a ce  a majalisar gudanarwa ta kungiyar Cisilac da suka hada guuiwa da gidauniyar Firiderich Ebert ta kasar Jamus suka shirya taron na mai bayyana cewa.

Yi wa matsalar daukan sakainar kashi da nuna abinda ya sahfi  wani sashi matsalarsu ce shi kadai. Farfesa  Isaac Albert  masani a fanin tsaro da ya gabatar da kasida yace an dade da baro shiri.

Samar da manufa ta bai daya tare da mikata ga gwamnati na iya zama mafita ga wannan matsala da a yanzu ta shafi kusan daukacin yanayin zamantakewa, ilimi tsaro da ma walwar jama'a