Karuwar annobar kwalara a Yemen | Labarai | DW | 22.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karuwar annobar kwalara a Yemen

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tare da wasu kungiyoyin agaji sun sake yin kashedi dangane da yaduwar da annobar kwalara ke ci gaba da yi a kasar Yemen.

A cewar hukumar, matsalar ka iya zarta wadda ta faru a kasar Haiti da ke matsayi mafi muni tun a shekara ta 2010. Ta ce babu alamun shawo kan annobar ya zuwa yanzu, musamman ma yadda damina ke kara ta'azzara lamarin, a cewar mai magana da yawun MDD a Yemen din, Farhan Haq.

Ita ma kungiyar agaji ta OXFAM wadda ke da cibiya a Birtaniya, ta ce wannan shi ne yanayi mafi muni da aka taba gani a tsukin shekara guda. Sama da mutum dubu da 800 ne dai cutar ta halaka yayin da wasu dubu 370 kuwa suka kamu, daga watan Afrilun zuwa wannan lokacin.