Karshen ayyukan dakarun NATO a Afghanistan | Labarai | DW | 28.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karshen ayyukan dakarun NATO a Afghanistan

Dakarun kungiyar tsaro ta NATO na Isaf da ke fafatawa tsawon shekaru 13 da 'yan kungiyar Taliban a Afghanistan, sun saukar da tutarsu a wannan Lahadi a wannan kasa.

Hakan ya kawo karshen ayyukan dakarun na NATO na Isaf a kasar ta Afghanistan, da har yanzu ta ke ci gaba da fuskantar kalubanen 'yan Taliban. Babban komandan dakarun na kungiyar tsaron ta NATO a kasar ta Afghanistan, Janar John Campbell, cikin jawabinsa ya yi bitar ayyukan da suka yi a wannan kasa, inda ya ce su na tare ne da nasara, sanna kuma ya ce, sun fitar da 'yan kasar daga cikin yanayi na zullumi da rishin mokama ta gari, kuma sun basu damar yin kyaukyawan fata na makoma ta gari a nan gaba. A ranar daya ga watan Janeru ne dai dakarun da zasu ci gaba da bayar da horo ga sojojin kasar ta Afghanistan, zasu maye gurbin wadannan dakaru na yaki.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu