Karnuka a fagen Daga
Shugaban Amirka Donald Trump ya wallafa hoton wani Kare na sojoji da ya sami rauni a farmakin kamo shugaban IS Abu Bakr al-Baghdadi. Karen wanda ba a baiyana sunansa ba, ba shi ne na farko da ya yi suna a fagen daga ba.
'Kare mai kwazo' na fadar White House
Shugaba Trump ya wallafa hoton wani kare jinsin Malinois na kasar Belgium wanda aka raunata a farmakin da ya halaka Abu Bakr al Baghdadi a Siriya. Ba a baiyana sunan karen ba domin yin hakan zai sa a gane wanda ke kula da shi da kuma rundunar da ta kai farmakin. Sai dai Reuters ya ruwaito cewa karen ya ji rauni kadan ne kawai kuma har ya koma bakin aiki. Trump yace karen ya yi babban aiki.
Rin Tin Tin, gwarzon yaki kuma tauraron fina finai
An dade tsawon shekaru ana amfani da karnuka a fagen yaki. Rin Tin Tin kare ne jinsin Shepherd na kasar Jamus da ya yi aiki a rundunar sojin Jamus a lokacin yakin duniya na daya wanda kuma sojojin Amirka suka kama shi, daga baya ya koma rundunar sojin Amirka. Rin Tin Tin ya shafe tsawon rayuwarsa a rundunar sojin Amirka. Ya cigaba da rayuwa mai nagarta a fagen fina-finan Hollywood a shekarun 1920
Samanja Jiggs, sojin Amirka
Wasu karnuka a fagen fama ba kasafai ake musu linzami ba kamar Rin TinTin. Jiggs kare ne gadanga kusar yaki wanda ya kasance kare na farko mai baiwar sa’a na sojin ruwan Amirka a 1922. Jiggs ya rika samun girma cikin hanzari inda ya zama Samanja cikin shekaru kalilan abin da ke zama babbar nasara ga sabon kurtu. An yi wa Jiggs cikakken faretin girmamawa ta soji bayan rasuwarsa a 1927
Ana fara bada horon tun haihuwa
Yawancin karnukan soji ana ba su horo tun suna ‘yan kwikwiyo. A rundunar sojin Jamus, ‘yan kwikwiyon kan kasance tare da masu horars da su har sai sun girma yadda za su fara aikin soji. A nan shugaban kasar Austria Alexander Van der Bellen yana rike da wani dan kwikwiyo da ke samun horo a rundunar sojin Austria.
'Robby's Law' ya sauya makomar karnukan soji
A shekarar 2000 shugaba Bill Clinton ya sanya hannu kan dokar “Robby” domin tabbatar da cewa karnuka a rundunar sojin Amirka ba a yi watsi da su a fagen yaki ko a kashe su saboda ko rauni ko rashin lafiya ba. A Vietnam karnuka 2,700 na sojin Amirka aka bai wa sojin kudancin Vietnam sannan aka kawar da guda 1,600. A yanzu Amirkawa masu horas da karnukan na iya rikonsu idan sun yi ritaya.
German Shepherds — Karnuka asalin Jamus
Duk da yanayin kyawunsu ba kowane sojan kare ne yake tsatson Shepherd ba. Sai dai wani bincike na Barkpost ya nuna kashi 85 cikin dari na karnukan soji a Amirka an sayo su ne daga kasashen Jamus da Netherlands bayan samun horo a can. German Shepherd shi ne jinsin da aka fi shahara yayin da Malinois na Belgium kamar wanda Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter ake samun su a ko'ina.