1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Sudan ta kudu ya samu karin wa'adi

Zulaiha Abubakar
July 12, 2018

'Yan majalisar dokokin Sudan ta kudu sun ka'da wata kuri'a a yau alhamis data sahalewa gwamnatin shugaba Salva Kiir samun karin wa'adin shekaru uku a shugabancin kasar a yunkurin su na kawo tsaiko cikin batun sulhu.

https://p.dw.com/p/31LEh
Südsudan Präsident Salva Kiir
Hoto: Reuters/M. N. Abdallah

Wannan kuri'a na zuwa ne lokacin da kasar Sudan ta yi Allah wadai da sukar da kungiyar Tarayyar Turai tayi wa kasashen Yuganda da Jibuti sakamakon karbar bakuncin Shugaba Omar al-Bashir na Sudan wanda kotun manyan lafuka ta Duniya da ke birnin Hague ke nema, kamar yadda ofishin ministan harkokin wajen kasar Sudan ya sanar a yau Alhamis.

Sanarwar ta kara da cewar tuni fadar mulkin kasar ta yi kiran jakadan kungiyar Tarayyar Turan don bayyana takaicin ta game da irin matsin lambar ta kungiyar tarayyar Turai ke yiwa kasashen Afrika akan su amince da zargin da kotun manyan laifukan ke yi wa kasar ta Sudan.

A makon daya gabata ne dai shugaba al-Bashir ya ziyarci kasar Uganda don gudanar da wani muhimmin taro tare da takwaransa na kasar Yoweri Museveni da kuma shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu don shirya yarjejeniyar da za ta kawo karshen yaki a Sudan ta kudu.