Karin tallafi na nemo ′yan matan Chibok | Labarai | DW | 11.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karin tallafi na nemo 'yan matan Chibok

Izra'ila ta yi tayin tallafawa tarayyar Najeriya wajen ganin an kubuto da 'yan matan nan sama da dari biyu da 'yan Boko Haram suka sace a jihar Borno da ke arewacin kasar.

Firaministan Izra'ilan Benjamin Netanyahu shi ne ya yi wa Najeriyar wannan tayin a wata zantawa da suka yi da shugaba Goodluck Jonathan ta wayar tarho a wannan Lahadin, inda ya ce kasarsa ta kadu matuka dangane da sace 'yan matan da aka yi.

Mr. Netanyahu ya ce baya ga taimakon da za su bada wajen kubuto da 'yan matan, kasarsa za kuma ta agaza wajen ganin an karya tashin bayan tada kayar bayan a kasar sai dai bai yi karin haske kan irin na'in tallafin da za su bada ba.

Gabannin wannan tayi na Izra'ilan dai, Amirka da Burtaniya da China sun daura aniyar yin aiki tare da jami'an tsaron Najeriya wajen gano inda 'yan matan na Chibok suke da nufin kubuto da su.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Ummaru Aliyu