1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da karin iskar gas daga Najeriya zuwa Turai

Uwais Abubakar Idris SB)(ZMA
April 12, 2022

Kungiyar tarayyar Turai ta bayyana bukatar kara yawan makamashin iskar gas da take saye daga Najeiya sakamakon kutsen Rasha a Ukraine da ya sanya nahiyar Turan neman hanyar cike gibin iskar gas da take saya daga Rasha.

https://p.dw.com/p/49qqj
Symbolbild | Nigeria Gaspipeline
Hoto: Florian Plaucheur/AFP/Getty Images

Kungiyar tarayyar Turai ta bayyana bukatar kara yawan makamashin iskar gas da take saye daga Najeiya biyo bayan yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine da ya sanya nahiyara turan neman hanyoyin cike gibin iskar gas din da take saye daga Rasha. Shin Najeriyar na da karfin ikon cimma buktara nahiyar Turan duk da alfanun da ta hango a ciki?

Kungiyara Tarayyar Turan dai na Karin matsin lamba da ma lalashi ga Najeriyar a kan batun samun Karin makamashin iskar gas daga kasar, inda sau biyu a jere jakadar kungiyar tarayyar turai a Najeriya Samuela Isope tana ganawa da jami'an gwamnatin Najeriyar a kan wannan batu. Kasashen kungiyar Tarayyar Turan na son adadin gas din da Najeriyar ke sayar masu ya zarta kasha 40 na makamashin iskara gas da take fitarwa zuwa kasashensu. Timipre Sylva shi ne ministan kasa a ma'aikatar kula da harkokin man fetir ta Najeriyar, wanda yake cewa kasar ta shirya.

Karin Bayani: Najeriya: Za a ci gaba da sayan mai a kan Naira 162.5

Symbolbild | Nigeria Gaspipeline
Hoto: Florian Plaucheur/AFP/Getty Images

Duk da dimbin albarNajeriya: Za a ci gaba da sayan mai a kan Naira 162.5 akar makamshin iskar gasa da Najeriya ke da shi na sama da cubic mita trilliyan 200, iskar gas da take fitarwa ba takai matakin da ake bukata ba. Ko bisa wannan kafa Najeriyar za ta iya cimma bukatar kasashen Turai? Muhammad Saleh Hassan kwarrare ne a fanin makamashin iskar gas da man fetir a Najeriya, wanda yake ganin kasar ya dace ta zabura.

Wannan kafa da ta budewa Najeriyar a lokacin da kasar ke aiki na shinfida bututun iskar gas zuwa Aljeria don isa ga Turai, a lokacin da tattalin arzikin Najeriya ke buktar sabbin hanyoyin samun kudadde daga waje.

Tun daga lokacin da yaki ya barke a tsakanin Rasha da Ukraine ne dai ake samun sauyi na siyasar duniya bisa ga guguwar da ke chanzawa, abinda Dr Abubakar Umar Kari masanin a kimiyyar siyasa ya ce lamari ne da ke da bangarori biyu.

A yayin da Najeriya ke zumudi amma ‘yan kasar na fatan gani a kasa kar a yi masu fafalolo, za a sa ido a ga kara matsawa ne zuwa ga kasashen Turan ko kuwa bukatar kasar ta dauki mataki na nesa da kasar Rasha zai iya biyo baya, domin inda baki ya karkata a nan miyau ke zuba.