Karin albashi har yanzu ana jika a Najeriya | Siyasa | DW | 24.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Karin albashi har yanzu ana jika a Najeriya

A rikicin da ke tsakanin gwamnatocin tarrayar Najeriya da ma’aikatan kasar, gwamnatin kasar ta kafa wani kwamitin mutane 29 da ta dorawa alhakin tattauna batun sabon karin albashin ma’aikata a kasar.

Tun a cikin watan Mayun bara ne dai ma'aikatan kasar suka mika wata bukatar karin albashin da ya kai na kusan Naira 56,000 ga gwamnatin da nufin rage radadin janye talafin man fetur a kasar. An dai dauki lokaci ana tattaunawa a tsakanin ma'aikata da gwamnatin kafin mika wani rahoto ga gwamnatin kasar a cikin watan Apfrilun da ya shude.

To sai dai kuma sai da yammacin Laraban nan ne dai gwamnatin kasar ta fitar da wani kwamiti na mutane 29 da zai kunshi  wakilai guda biyar daga bangare na gwamnatin tarrayar, sannan kuma da gwamnonin kasar guda shida game da wakilan kungiyoyi na kwadago takwas sannan kuma  da kungiyar masana'an tu da samar da aikin yi ta NECA da ita ma aka dorawa alhakin samar da wakilan guda takwas.

Ana dai sa ran tafka dogon turanci da ma muhawara a tsakani na gwamnatin da ke korafin rashin kudi da ma jihohi na kasar da  damansu ke tatata ga biyan albashin yanzu, da ma ma'aikatan da ke fadin tsada ta rayuwa ta cinye albashin da nufin cimma daidaito na sabon albashin da za'a mika shi ga majalisun kasar biyu.

Chris Ngige dai na zaman ministan na kwadagon kasar, da kuma ya ce sun yanke hukuncin jawo kowa da nufin kaucewar rikici na bani na iya cikin kasar.

" A lokacin da zababbun ‘yan kwamitin suka hadu , muna san rantsar dasu a kwanan nan, ‘yan kwadago zas u mika bukatarsu ta  Naira 56,000 a matsayin mafi karancin albashi domin tattaunawa da bangarori kamar yadda doka ta kwadago a kasar ta aiyyana. A lokacin kuma masu biyan albashin za su fadi abun da suke iya biya. Alal misali kungiya ta masu daukar aiki ta ce ba zata iya biyan sabon albashin ba saboda hakan na nufin karin albashi har ya zuwa sama, wannan tattaunawa za'a yi ta ne a teburin tattaunawa.”

To sai dai kuma ko ya zuwa yaushe ne bangarorin ke iya kaiwa ga amincewar da ta kai ga sabon albashin dai, tattaunawar ta na zuwa ne a dai dai lokacin da tattalin arzikin tarrayar Najeriyar ke nuna alamun harbawa.

Gwamnatin kasar dai ta ce ta gamsu da wata sabuwar kiddidigar da ke fadin tattali na arzikin kasar ya ragu da kusan rabin kashi a zangon farko na shekarar bana.

 

Sauti da bidiyo akan labarin