Karancin sabbin kudi ya haifar da zanga-zanga a Najeriya
February 8, 2023Talla
Rashin sabbin kudi da al'umma ke fuskanta tun bayan da aka sake fasalta wasu takardun naira a kasar da ke ci gaba da janyo dogayen layi a bankuna ya fusata masu boren.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ta Ogun Abimbola Oyeyemi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar zanga-zangar ta barke a wasu garuruwa 3 na jihar, inda masu boren suka farfasa wasu bankuna biyu tare da kona tayoyi a kan tituna.
Wannan na zuwa ne kasa da makwanni uku kafin al'ummar kasar su garzaya rumfunan zabe, Najeriya kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka na fuskantar karancin sabbin kudin a yayin da aka daina karbar tsofafin, kazalika ana fuskantar karancin man fetur,
Ko a makon da ya gabata an gudanar da bore a wasu manyan garuruwan kasar.