Karancin kudin taimako ga yankunan girgizar kasa a Pakistan | Labarai | DW | 08.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karancin kudin taimako ga yankunan girgizar kasa a Pakistan

Sama da makonni 4 bayan aukuwar mummunar girgizar kasa a arewacin Pakistan, MDD da kungiyar ba da agaji ta Red Cross da takwararta ta musulmi sun sake yin kira ga gamaiyar kasa da kasa da ta kai taimakon gaggawa. Wakilan kungiyoyin sun nunar da cewa idan ba´a hanzarta cika alkawuran da aka dauka na ba da isassun kudade ba, to mutane masu yawan gaske ka iya mutuwa saboda sanyin hunturun da ke dada karatowa. Shi ma a nasa bangaren babban jami´in dake kula da taimakon jin kai na MDD Jan Egeland yayi kira da aka samar da injunan dumama daki baya ga barguna da ake bukata ruwa ajallo a yankunan da gurgizar kasar ta fi yin muni. Alkalumman baya-bayan nan da ma´aikatar kudi a birnin Islambad ta bayar sun nunar da cewa yawan wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar ta ranar 8 ga watan oktoba yanzu ya kai mutum dubu 86 a Pakistan kadai.