Karanci mai ya kusa durkusar da Najeriya | Siyasa | DW | 28.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Karanci mai ya kusa durkusar da Najeriya

Karancin albarkatun man fetur da aka yi fama da shi a Najeriya ya yi kokarin durkusar da harkokin kasuwanci a kasar. Lamarin ya jawo asarar miliyoyin Naira ga 'yan kasuwa.

Karancin man fatur da Najeriya ta fuskanta biyo bayan yajin aikin da dillan da ke dakon mai suka yi ya jefa Najeriya cikin mawuyacin hali. Lamarin dai ya jawo asara mai dimbin yawa ga 'yan kasuwa. Sai dai daga bisani gwamnati da dillalan man fetur din daidaita har ma sun koma dakon mai din kamar yadda aka saba.

DW.COM