Matsalar karancin man fetir a Najeriya | Siyasa | DW | 21.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar karancin man fetir a Najeriya

Karancin man fetur na haddasa hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kasuwanni tare da haddasa durkushewar kamfanoni a Najeriya

Yanzu haka dai hada-hadar harkokin kasuwanci tsakanin manya da Kannanan 'yan kasuwa da su kansu masu sayayyan kayayyakin na fuskantar babban kalubale da komabaya a fadin kasar sabili da matsalar karancin man fetur.
Alhaji Adamu maishinkafa na dai zama daya daga cikin shuwagabannin kungiyoyin 'yan kasuwa a Nigeria dake bukatar ganin Gwamnatin tarayar ta hanzarta daukar matakan gaggawa domin shawo kan wannan lamari .

" Kama tun daga sayan kayayyakin abunci da Sitorori da wasu kayayyakin gine-gine dukkanin wadannan abubuwa sun yi tashin gwauran zabi a kasuwannin kasar,yace muna ganin cewa lallai dai kam akwai gagarumar gudun mawar da Hukumomi za su bada wajan shawo kan wannan lamari,domin ceto alumma daga matsatsin rayuwa da alumman kasar suka fada ciki "

Benzin Afrika

Kasuwar man Fetir ta bayan fage na taimakawa ga haddasa hauhawar farashin man fetir

Korafin 'Yan kasuwa kan tsadar man fetir

A wannan karan ma dai hatta Hukumar da Gwamnati ta kafa domin kulawa da harkokin kasuwanci anan Kaduna ita ma ta koka dangane da irin matsatsin rayuwa da jama'a suka fada sanadiyyar wannan matsala da ta haddasa hauhawar farashin kayayyakin kasuwannin.

Su kuwa Masana Kimiyya da fasahar zamani kira ne suka yi ga Hukumomin kasar wajan Rage dogaro kan man fetur,domin fara anfani da wasu makamashin na samar da wutar lantarki. Mallam yahaya Ahmed shine shugaban kungiyar developmental association for renewable energy:

Shawarar masana kimiyyar lantarki

Benzin Afrika

Matsalar karancin man fetir na tasiri wajan tauye tafiyar harakokin yau da kullu

"Akwai jihohin guda 2 da ya kamata gwamnati ta fara tunanin anfani da fiyalen saharan wadannan wurare domin samar da makamashi marasa gurbacewar yanayi,yace mudden gwamnati za ta tashi tsaye wajan taimakawa ta hanyar anfani da hasken rana don samun makamashi marasa gurbacewar yanayi,hakan zai taimaka ainun wajan shawo kan matsalar rashin man fetur da wutar lantarki dake addabar Nigeria"

Ya zuwa wannan lokaci dai a sabili da matsalar karancin wutar lantarki da rashin manfetur ,kanana da matsakaitan 'yan kasuwa da damar gaske ne suka koma zaman kashe wando,lamarin dake zama wata barazana ga yunkurin da hukumomi da kungiyoyin ke yi na samun tabbataccen tsaro da ci-gaba a cikin kasar

Sauti da bidiyo akan labarin