An shawo kan matsalar rashin man fetur a Najeriya | Labarai | DW | 25.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An shawo kan matsalar rashin man fetur a Najeriya

Ma’aikatan kamfanin kula da albarakatun man fetir na NNPC na Najeriya sun janye yajin aikin suka shiga wanda ya haifar da karancin mai da raguwar wuta lantarki a kasar.

To kusan komai dai ya kama hanyar tsaya cik a Najeriyar , kama daga bankuna da mafi yawansu karancin man diesel ya tilasta su rufewa daga karfe daya na ranar litinin nan, ya zuwa kamfanonin sadrawa da suke gargadi cewa bisa dole zasu rufe hanyar sadarwa, bata gidajen jama’a ake yi bad a mafi yawansu suka kwashe kwanaki babu wutar.

Duk wannan matsala ce ta yajin aikin ma’aikatan kamfanin main a NNPC da ta shafi harkar samar da wuta lantarkin kasar, domin rashin iskar gas ta sanya wutar raguwa daga sama da megawatt dubu hudu zuwa 1300 ga kasar. To ko wacce illa wannan hali da kasarv ta afaka a ciki ked a shi ga tattalin arzikin Najeriyar? Mallam Abubakar Ali masanin tattalin arziki ne a Najeriyar.

'’Ai ba karamin asara aka yi, domin harkokin ana zuwa hada hada a banki a ajiye kudi a fitar da su, tilas ya shafi tattalin arziki, domin a gaskiya halin da aka shiga na La haula ne don idan ha duba rashin man nan ya kawo matsala inda wasu ma’aikatu na tunanen su rife wasu su rage ma’aikata, don haka ya kawo matsala ga kowa da kowa’’.

Munin da wannan lamari ya yi ya sanya kwamitin majalisar datawan Najeriya mai kula da harkokin mai shiga cikin lamarin, inda bayan zaman da suka yi ma’aikatan kamfanin na NNPC suka amince da janye yajin aikin tare da alkawarin ci gaba da rarraba mai a Najeriyar. Alhaji Abubakar Mai Kandi shine mataimakin kungiyar yan kasuwa masu man fetir wanda ya hallarci zaman day a kaiga janyae yajin aikin.

‘’To abin da zai nuna yanzu to wahalar da ake ciki a yan kwanakin nan da alama za’a samu sauki, Mu kanmu hankalinmu ya tashi a kan halin da ake ciki, don haka yajin aikin da aka janye ya yi mana dadi sosai’’.

Sauti da bidiyo akan labarin