1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kara sojoji a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya

April 1, 2014

Rundunar sojin ta zartar da hakan ne sakamakon karuwar rigingimu da ke da nasaba da fadan kabilanci da ya haddasa asarar rayuka a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/1BZo7
Nigeria Soldaten
Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

A wani abun da ke zaman kokarinsu na shawo kan karuwar tashe tashen hankulan da ke neman yamutsa lamura a jihohin Benue da Plateau da 'yar uwarsu ta Nasarawa, rundunar tsaron kasar sun aiyyana tura karin soja da jami'an tsaro da nufin tunkarar 'yan ina da kisan da ke kisa suna shanye jini a cikin yankin na Arewa maso Tsakiya.

Babu dai zato ba kuma tsammani karamar magana ta kai ga girma da tada hankula a jihohin Benue da Plateau da 'yar uwarsu ta Nasarawa da suka zauna suka kalli tashe tashen hankali da zubar da jinin da babu irin sa a yankin a lokaci mai dama.

An dai kai ga kona kauyuka an kuma tarwatsa al'umma a cikin sabon rikicin daya faro tare da satar shanu kafin daga baya ya koma wani dandalin 'yan ina da kisan da ke farma Sarakuna suna hana talakawan yankin bacci.

Abun kuma da ya kai ga fadar gwamnatin kasar mai da martani tare da jibge karin soja cikin yankin da nufin kwantar da hankula da ma kila kawo karshen maharan da ke barazanar mai da yankin Arewa ta Tsakiyar kasar wani sabon dandalin rikici ga kasar da ke fuskantar karuwar tashin hankali a Arewa maso Gabas.

Nigeria Soldaten
Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

Sabon matakin sojan da ke zaman irinsa mafi girman tun bayan kara ta'azzarar rikicin a farkon shekarar da muke cikin dai, na zuwa ne a dai dai lokacin da rahotannin da ke fitowa daga yankin na ambato yiwuwar amfani da guba wajen kisan a kalla mutane 200 a cikin jihar Benue da ke zaman hedikwatar rikicin.

Duk da cewar dai mahukuntan jihar basu fito domin bayyana irin gubar ko kuma tasirin ta cikin rikicin ba an dai ruwaito kakakin gwamnatin jihar Justine Amase na fadin rashin ganin alamar rauna a jikin wasu mattatu kusan dari biyu ya sanya gwamnatin kaddamar da bincike da nufin tabbatar da ko an kai ga basu guba ne a gabar kogin Benue da ya ratsa jihar.

To sai dai kuma a nan Abuja gwamnan jihar Gabriel Suswan da ya gana da shugaba Jonathan yace matakai sun yi nisa da nufin tabbatar da karshen rikicin da ke barazanar tarwatsa lamura a daukacin yankin na arewa maso tsakiya.

"Ina farin ciki da ganawata da shugabannin Fulani a daukacin daren jiya, sun kawo shawara kuma na amince cewar akwai bukatar kafa runduna ta hadin gwiwa tsakaninsu da mu Manoma ba wai kawai na Tiv ba, da nufin gano masu kai mana wadannan hare hare, saboda sun shaida mun cewar wadannan mutane na yi musu barazana suma. Na kuma gamsu da matakai kwarara da shugaban kasa ke dauka."

Ana dai kallon sabon matakin hada karfi da ma na karfe a tsakanin manyan abokan wasan da suka rikide ya zuwa gaba a tsakanin juna dai, a matsayin wani sabon babin da ke iya kai wa ga warware matsalar da ma kila sake tabbatar da zaman lafiya ga al'umarsa da ke da matukar muhimanci ga gwamnatin ta Abuja yayin zabe.

To sai dai kuma a fadar Labaran Maku da ke zaman kakakin gwamnatin ta Abuja dai batu na hadin kan al'umma na zaman babbar mafita maimakon karfi na hatsin da a baya ya gaza kaiwa ga ganin bayan masu harin.

Nigeria Flüchtlinge aus Borno
Hoto: DW

"A cikin Nasarawa ana nan ana bata kashi. Kullum ko ka shiga Nasarawa yanzu ko ka shiga Doma ta bayan garin Doma ana fitina , in ka je ta bayan garin Awei ana fitina, in ka dubi Benue Cross Over ana fita. In ka duba an tura sojoji da jami'an tsaro an tura sojoji a Benue da Nasarawa kuma da izinin Allah za'a samu nasara. Amma gaskiyar magana ita ce dole ne shugabanni su hada kawunan mutane".

To sai dai kuma in har sabuwar dabarar hada karfi don aiki tare na iya kawo karshen matsalar rashin tsaron yankin Arewa ta Tsakiya, can a Arewa maso Gabas din da karfin hatsi ke zaman hanyar zabi ta gwamnati, sojan kasar sun ce a kalla wasu 'yan kungiyar ta Boko Haram hudu ne bam ya tashi da su a kan hanyarsu ta zuwa wani gidan mai a birnin da nufin tada bama bamai.

Abun kuma da ya kai ga rufe daukacin hanyar da ta hada birnin Maiduguri da jihar Yobe ta kuma kai ga mummunan cunkuson motoci ga masu kokarin shiga birnin har ya zuwa yammacin wannan Talatar.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar