1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kanada ta yi watsi da bukatar 'yan Afirka ta shiga kasar

Lateefa Mustapha Ja'afar ZUD
July 29, 2022

Mutanen Afirka da ke son halartar babban taron duniya kan yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDs ko kuma SIDA da ke gudana a kasar Kanada, na kokawa kan yadda Kanadan ta hana wasunsu izinin shiga kasar.

https://p.dw.com/p/4EtHo
Kanada World AIDS Conference
Hoto: THE CANADIAN PRESS/Ryan Remiorz/empics/picture alliance

Wannan dai shi ne karo na 24 da ake shirya irin wannan taro, kuma an shirya shi da nufin duniya ta hada hannu waje guda domin shawo kan wannan cuta.  
Taron na hada dubban masana kimiyya da 'yan siyasa da masu rajin kare hakkin dan Adam da kuma ma'aikatan bayar da agaji a kokarin kawo karshen cutar mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDs ko kuma SIDA . Sai dai kuma matsalar rashin samun takardar izinin shiga kasar ta Kanada wato Visa, ka iya hana 'yan Afirka halartar taron na bana.


Philomena Gori na zaman guda daga cikin ma'aikatan agaji da ke bayar da taimako ga wadanda suka kamu da cutar a Kamaru, sai dai bayan ta kashe kudin kimanin dalar Amirka 2000 domin samun damar halartar taron da aka fara gudanarwa a Jumma'ar nan, hakarta ta gaza cimma ruwa. Bayan tsawon kwanaki 88 da kammala duk wani mataki da aka bayyana na samun takardar izinin shiga Kanada, mako guda gabanin taron, Gori ta samu takardar cewa ba a amince da bukatarta ta zuwa Kanada domin halartar taron na yaki da cutar HIV/AIDs ko kuma SIDA ba. A hirarta da  tashar DW kan lamarin cikin fushi ta ce ''Na ji takaici matuka, a yanzu haka ina cikin bacin rai. Na yi kokari sosai domin ganin na samu halartar wannan taron, domin in samo wani abu da zan taimaki al'ummata in na dawo gida.'' Ta ce a Afirka aka fi kamuwa da HIV/AIDS, don haka ta tsammaci Kanada za ta ba 'yan Afirkan dama fiye da kowa. 

'Yar Kamaru Philomena Gori da Kanada ta ki ba izinin zuwa taron HIV/AIDS
'Yar Kamaru Philomena Gori da Kanada ta ki ba izinin zuwa taron HIV/AIDSHoto: privat

Ba Gori ce kadai ta fuskanci wannan kalubale ba, domin kuwa shi ma dan rajin wayar da kan matasa Sam W. Pionlay dan asalin Laberiya da ke karatu a Maroko ya samu gayyata daga kungiyar masu dauke da kwayar cutar ta HIV/AIDs ko kuma SIDA ta duniya. Cocin Delaware ta dauki nauyin zuwansa Kanada, sai dai a ranar 19 ga wannan wata na Yuli da muke ciki, ya samu takarda daga mahukuntan Kanada da ke nuni da cewa ba za su amince da shigarsa kasar ba domin ba su da tabbacin zai koma Maroko wajen karatunsa bayan kammala taron. 


Wannan matsala dai ta janyo yin suka kan zabar kasar da za a gudanar da taron. David Ndikumana shi ne daraktan kungiyar WEKA da ke rajin kare hakkin masu auren jinsi da 'yan tsiraru da kuma masu dauke dacuta mai karya garkuwar jiki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ya shaidawa DW cewa mutane biyu daga kungiyarsa sun samu katin gayyata sai dai har yanzu ba su san makomarsu ba.  

David Ndikumana daraktan kungiyar WEKA da ke rajin kare masu HIV/AIDS a Kwango da Kanada ta hana shiga kasarta.
David Ndikumana daraktan kungiyar WEKA da ke rajin kare masu HIV/AIDS a Kwango da Kanada ta hana shiga kasarta.Hoto: privat


"Abin da zan iya cewa shi ne, Kanada na nuna wariya. Mun tambaya mun kuma rubutawa Hukumar Kula da Masu Dauke da Cutar AIDs ta Majalisar Dinkin Duniya UNAID, domin jin dalilin da ya sa Kanada ce kawai za ta dauki nauyin taron? Mai ya sa ba za mu sauya lokacin taron ba?" Cikin bacin rai Ndikumana ya yi wadannan tambayoyi.