Neman mafita a kan HIV AIDs ko SIDA | Siyasa | DW | 22.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Neman mafita a kan HIV AIDs ko SIDA

Kammala taron kwararru da masana kimiyya na kasashen duniya a birnin Durban na Afirka ta kudu da nufin samar da hanyoyin kawo karshen cuta mai karya garkuwar jiki, HIV AIDs ko kuma SIDA.

Zauren taron neman mafita ga cutar AIDs ko SIDA a birnin Durban na Afirka ta Kudu

Zauren taron neman mafita ga cutar AIDs ko SIDA a birnin Durban na Afirka ta Kudu

Taron wanda aka soma gudanar da shi tun a shekarun 2000 a wannan jikon an samu ci gaba sosai, ko da yake ma adadin masu kamuwa da ciwon na AIDS ko SIDA a kowace shekara bai sauya ba. Mutane miliyan biyu da rabi ne ke kamuwa da kwayoyin cutar ta HIV AIDs ko kuma SIDA a kowace shekara a duniya, adadin kuma da kwararru suka ce har yanzu bai yi kasa ba a cikin shekaru 10 da suka gabata wanda aka tabbatar da cewar a kowace rana mutane 7,000 ke kamuwa da wannan cuta.

Gangamin yaki da cutar AIDs ko SIDA yayin taron Durban

Gangamin yaki da cutar AIDs ko SIDA yayin taron Durban

Tsakanin shekarun 2005 zuwa 2015 alkaluma na sababbin mutane da suka kamu da ciwon na AIDs ko SIDA ya karu a kasashe 74 na yankin Asiya da Arewacin Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya da Gabashin nahiyar Turai da kuma wasu kasashe na Yammacin Turan irinsu Spain da Girka.

Karuwar masu dauke da cutar

Bincike ya nuna cewar a shekara ta 2015 mutane miliyan 38 ne ke dauke da kwayoyin cutar a duniya sabanin shekarun 2000, inda mutane miliyan 28 ne kadai ke dauke da cutar ta AIDs ko kuma SIDA. Sai dai sakamakon yadda ake daukar dawainiyar masu fama da ciwon adadin masu mutuwa ya ragu a shekara ta 2015 fiye da shekara ta 2005.

Likitocin da suka sadaukar da rayuwarsu wajen duba marasa lafiya

Likitocin da suka sadaukar da rayuwarsu wajen duba marasa lafiya

Doctor Eric Goemaere, na kungiyar Likitoci na Gari na Kowa, wato Doctors Without Boders ko kuma Médecins Sans Frontières ya ce har yanzu da sauran aiki a gaba musamman ma a nahiyar Afirka. A yayin wannan taro da aka gudanar Durban na Afirka ta Kudu dai, an gabatar da sababbin fasahohi na yaki da cutar wacce kawo yanzu ta lakume rayukan mutane miliyan 30 tun daga shekara ta 1980.

Gaza cimma kudirin 2020

Wani hadin magani da ake bayarwa mai suna ARV wanda ya kunshi magunguna daban-daban na taimakawa wajen kara tsawaita rayuwar masu fama da ciwon na HIV AIDs ko kuma SIDA. To amma duk da wannan kokari hukmar yaki da cutar ta AIDs ko SIDA a duniya ta Majalisar Dinkin Duniya ONUSIDA, UNAIDS ta ce yawancin kasahen duniya ba za su iya cimma kudirin yaki da cutar kafin nan da shekarun 2020 ba.

Sauti da bidiyo akan labarin