An soma taron yaki da cutar HIV/AIDS | Labarai | DW | 23.07.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soma taron yaki da cutar HIV/AIDS

Masana ilimin kimiyya kusan dubu 18 sun hallara a birnin Amsterdam domin gudanar da taro na tsahon kwanaki hudu kan yakar cutar HIV/AIDs ko Sida da ke janyo asarar rayuka na akalla mutane miliyan daya a kowacce shekara.

AIDS in Indien

Daga cikin mahalarta taron, akwai wasu fitattun mutane da suka hada da Bill Clinton tsohon shugaban kasar Amirka da Yerima Harry na Ingila da kuma mawakin nan Elton John. Wadannan mutane dai na daga cikin masu fafutuka na ganin an inganta rayuwar wadanda suka riga suka kamu da cutar da kuma fatan ganin an kawar da ita baki daya daga doron kasa.

Taken taron na bana da ke zaman karo na 22 tun bayan bullar cutar da ke ci gaba da yin barazana ga rayuwar al'umma., shi ne: ''Kawar da kyama da karfafa kaunar Juna". Majalisar Dinkin Duniya da ke fatan ganin bayan annobar nan da shekara ta 2030, ta bayyana fargaba kan yadda cutar ke kara yaduwa a wasu kasashen duniya.

Alkaluman majalisar na nuni da cewa, mutum miliyan daya da dari takwas ne suka kamu da cutar a bara, a yayin da mutum akalla miliyan 37 yanzu haka ke dauke da kwayar cutar a sassan duniya.Taron na birnin Amsterdam dai zai kara karfafa matakan ceton rayukan jama'a daga halaka sakamakon kwayar cutar.