Kamfanin Huawei ya yi watsi da zargin Amirka | Labarai | DW | 29.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamfanin Huawei ya yi watsi da zargin Amirka

Kamfanin ya ce bai yadda da jerin zargin laifuka da gwamnatin Amirkar ke zarginshi a kotu ba, na cewa ma'aiktanta na saba ka'idar kasuwanci da satar fasaha ba.

Fitaccen kamfanin kera wayoyin salula na kasar China Huawei, ya zargi Amirka da yi masa  karya na saba dokokin kasuwanci da aikata zamba a harkokin kasuwancin da ya ke yi a Amirka. Ma'aikatar shari'a ta Amirka ta ce kamfanin Huawei na satar bayanan fasaha da leken asirin kasuwanci, tare da yi wa bankunan Amirka karya. Katafaren kamfanin sadarwar Huawei ta zargi hukumomin Amirka da yin watsi da bukatar tattauna batun tsare wata babbar jami'ar kamfanin da aka tsare a kasar Kanada a shekarar 2018.