Kamfanin Dana Air ya koma zirga-zirga | Siyasa | DW | 04.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kamfanin Dana Air ya koma zirga-zirga

Duk da har yanzu ba'a kammala bincike game da sakamakon hadarin jirgin saman kamfanin Dana ba, Najeriya ta sake bashi izinin komawa daukar fasinjoji.

Wata sabuwar takadamma ta kuno kai a tsakanin majalisar dokokin Najeriya da gwamnatin kasar sakamakon maido da zirga-zirga kamfanin jiragen saman Dana Air wanda har zuwa wannan lokaci ba'a bayyana dalilan afkuwar hatsarin da ya yi dalilin mutuwar mutane 153, abinda ya sanya maida murtani mai zafi a kan inda aka dosa a kasar.

Sake maido da zirga-zirgar kamfanin jiragen saman Najeriyar na Dana watanni bakwai bayan da ya yi hatsarin da ya halaka mutane 153, ba tare da sanin zahirin sakamakon hatsarin ba, na zama babban dalilin day a sanya tada jijiyar wuyar da majalisar dokokin Najeriyar ke yi. Majalisar da ta fusata saboda yadda aka baiwa kamfanin izinin sake komawa ya ci gaba da zirga zirga a Najeriyar a daidai lokacin da ake ci gaba da bincike a kan wannan hatsari da ke zama daya daga cikin munanan hatsarin jirgin saman da aka yi a Najeriyar, saboda zargin sakaci da saba kaida da ake yi a kan lamarin. Hon Ibrahim Tukur El-Sudi dan majalisar wakilan Najeriya ne da ya bayyana yadda suka dauki wannan mataki.

Flugzeugabsturz in Nigeria

Hadurran jiragen sama sun zama ruwan dare a Najeriya

‘'Abin takaici ne a ce gwamnatin Najeriya ko kuma hukumar zirga zirgar jiragen sama ace sun basu izinin su fara zirgz zirga a Najeriya wannan ba daidai bane. Wannan ya nuna cewa har yanzu ita gwamnatin Najeriya bata yarda da cewa akwai majalisa ba, saboda mun ga abubuwan da ke faruwa ana cuwa-cuwa ainun a cikin al'ammuran, hukumomin da ya kamata su sa idannu basa yin hakan. Sai ka ga jirgi an bashi takardar binciken da ake yi daga lokaci zuwa lokaci, amma idan ka je sai kaga zahiri ba haka ba, takarda ce kawai aka bayar''.

Rashin aiwatar da sakamakon hatsururrukan jiragen saman da akan fuskanta a Najeriya saboda zagin cin hanci da rashawa na zama babbar matsalar da ake danganta shi da ci gaba da lalata tsarin sufurin jiragen sama a Najeriyar. To sai dai ga Sanata Hadi Sirki wanda kwararren matukin jirgin sama ne yace korafi akan fitar da sakamakon hatsarin jirgin saman ba karamin lamari bane, domin dole ne a yi shi a natse.

‘'Yace to shi wannan bakin akwati wata naura ce a cikin jirgin sama wacce take to in an dauko shi dama akan kaishi dakin bincike ne a buda shi a duba to mu har yanzu a nan babu masu wannan fasahar da zasu bude shi, don yawanci ai shi hatsarin jirgin sama ba wai haka kawai bam, yake faruwa matuki yace ya faru ba''.

Nigeria Flughafen Lagos Archivbild 2007

Tashar jiragen saman birnin Lagos a Najeriya

To sai dai kakakin hukumar kula da sufurin jiragen saman Najeriyar Sam Adurogboye ya bayyana cewa hukumar ta tabbatar da cewar kamfanin na Dana ya kammala sake tantancewar cancanta da aka tsara bisa mataki biyar kafin daukan matakin sake baiwa kamfanin iznin komawa bakin aiki. A yanzu da gwamnatin ta yi gaba wajen maido da kamfanin Dana bisa aikinsa a dai dai lokacin da mutanen da yan uwansu suka mutu a hatsarin jirgin ke jiran a biya su diyyar rasa yan uwansu, dama yadda lamarin harkar sufurin jiragen saman kasar ke ciki ya sanya tambayar matakin da majalisar zata dauka a kan wannan lamari. Har Ila yau ga Hon Ibrahim Tukur El- Sudi.

‘'Ina baka tabbacin majalisa zata dau mataki cikin gaggawa to zamu yi amfanio da wannan dama da iko domin mu tabbatar da cewa an yi abinda ya dace''.

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da aka fi fuskantan hatsarin jiragen sama a Afrika, inda sannu a hankali masu hannu da shuni ke mayar da malakar jirgi a matsayin abin kawa da isa a kasar da fiye da kasha sitin cikin dari na al'ummarta ke rayuwa a kasa da dala guda.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin