1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Kamfanin Boeing zai sallami ma'aikata 17,000

October 12, 2024

Kamfanin kera jiragen sama na Boeing ya fada cikin tsaka mai wuya sakamakon kura-kurai da aka samu a jiragen da ya kera a baya-bayan nan lamarin da ya jefa shi cikin matsi na karancin kudade.

https://p.dw.com/p/4liB5
Kamfanin Boeing zai rage kashi 10 cikin 100 na ma'aikatansa
Kamfanin Boeing zai rage kashi 10 cikin 100 na ma'aikatansaHoto: Richard Drew/AP/dpa/picture alliance

Kamfanin kera jiragen sama na Boeing ya sanar da cewa zai rage kashi 10 cikin 100 na ma'aikatansa a fadin duniya a cikin watanni masu zuwa, lamarin da ka iya shafar guraben aiki akalla 17,000. Kamfanin mallakin Amurka ya kuma ce yana duba tsaren-tsarensa na kera jirage a kokarin da yake na shawo kan matsalolin kudade da yake fuskanta.

Karin bayani: An hana Boeing 737 MAX shiga wasu kasashen

A cikin wasu sakonni guda biyu da ya aike, kamfanin kera jiragen saman ya ba da sanarwar cewa za a samu karin jinkiri wajen kammala kera sabon sunfurin jirginsa mafi girma 777X da kuma daina kera jirage sunfurin 767 a shekarar 2027.

Kamfanin Boeing dai ya fada cikin tsaka mai wuya ne sakamakon kura-kurai da aka samu a jiragen da ya kera a baya-bayan nan, musamman ma hadarin da wani jirgi kirarsa na kamfani Alaska Airlines ya yi a farkon watan Janairu na wannan shekara.