Boeing zai samar da manhaja ga jiragensa
March 28, 2019Kanfanin Boeing da ke kera jiragen sama ya bayyana sauye-sauyen da zai yi wa na'urar jirginsa samfurin Max na takwas wanda ya yi hadari a Indonesiya da Habasha a watannin baya. A gaban dimbin manaima labarai a cibiyarsa da ke birnin Renton na Amirka, kanfanin Boeing karkashin shugabanninsa ya ce zai sa wa jirgin wata manhaja da za ta rika gargadi matikar wata matsala ta kunno kai a lokacin tashinsa.
Boeing ya dauki wannan matakin ne domin kwantar da hankula kanfanonin jiragen sama da ke amfani da sanfurin MAX 8. Amma bai sanar da lokacin da jirgin zi koma bakin aiki ba tun bayan da aka dakatar da amfani da shi a sassa dabam-daban na duniya.
Mutane 346 ne suka rigamu gidan gaskiya a hadura biyu da sanfurin jirgi Max na takwas ya yi a Indonisiya da kuma a Habasha. Sai dai har yanzu masu bincike ba su gano dalilan da suka sa jiragen sanfurin Max na takwas suka rika rikitowa ba.