1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hana Boeing 737 MAX shiga wasu kasashen

Ahmed Salisu
March 12, 2019

Wasu kasashen duniya sun hana kamfanonin da ke da jirage kirar Boeing 737 MAX shiga sararin samaniyarsu baya irin jirgin ya yi hadari har sau biyu a tsukin watanni biyar.

https://p.dw.com/p/3EtiN
Großbritannien Boeing 737 MAX in Farnborough
Hoto: picture alliance/ZUMA Press/L. Faerberg

Kasashen da suka hada Birtaniya da Jamus da Faransa da Norway sun haramtawa kamfanonin jiragen sama da ke amfani da jirgin nan kirar Boeing 737 MAX shiga sararin samaniyarsu har sai kamfanin da ke kera jirgin ya kammala bincike tare da gano musababbin faduwar irinsa har sau biyu kasa da watanni 6.

Wannan haramci da kasashen suka yi dai ya biyo bayan hadarin da irin wannan jirgi mallakin kamfanin Ethiopian Airlines ya yi a ranar Lahadin da ta gabata inda dukannin fasinjojinsa 157 suka rasu bayan faduwarsa, 'yan mintoci kalilan bayan tashinsa daga birnin Addis Ababa na Habasha zuwa Nairobin Kenya.

Gabannin daukar wannan mataki da wadannan kasashe suka yi dai, kamfanonin jirage da dama ciki kuwa har da shi kansa Ethiopian Airlines din da Turkish Airlines sun sanar da dakatar da amfani da jiragensu kirar 737 MAX din. Haka ma abin yake ga kasar China da Brazil da Mexico da kuma Argentina wadda kamfanin zirga-zirgar jiragenta ke amfani da samfurin jiragen har guda 8.