Kamen manyan jami′an gwamnati a Saudiyya | Labarai | DW | 05.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamen manyan jami'an gwamnati a Saudiyya

Hukumomin Saudiyya sun kaddamar da kame-kamen wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da tsoffin ministoci a wani matakin yaki da cin hanci da masarautar ta kaddamar.

Daga cikin wadanda aka kama har da hamshakin mai arzikin nan kuma dan sarki a Saudiyya Al-Walid ben Talal. Hakan dai ya biyo bayan kafa wata hukuma ta yaki da cin hanci da rashawa a kasar ta Saudiyya wadda Yerima mai jiran gadon na Saudiyya Mohammed ben Salmane ke jagoranta.

A hannu daya kuma an kori wasu manyan ma'aikata daga mukamansu cikinsu har da Shugaban sojojin kundunbala na kasar Metab ben Abdallah da ake yi wa kallon yana daga cikin masu neman shugabancin masarautar, da kuma Shugaban sojojin Ruwan kasar Abdallah Al-Sultan da Ministan tattalin arziki Adel Fakih.

Yerima Mohammed ben Salmane dan sarki Salman na Saudiyya mai shekaru 32 da haihuwa, na ci gaba da karfafa ikonsa, inda a cewar gidan talbijin na Al-Arabiyya, baki daya an kama 'yan sarki 11 da ministoci hudu, gami tsoffin ministoci gwammai.